Najeriya: Barayin shanu 700 sun tuba a Kaduna

Shanu da Fulani

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Fulani makiyaya na korafin ana sace musu shanu

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta Najeriya ta ce ta sasanta da wasu daruruwan 'yan "ta'adda da barayin shanu" da suka addabi jihar.

A 'yan shekarun nan dai ana samun tashin hankali da kashe-kashen jama'a a jihar da ma wadansu jihohi makwabta.

Rundunar ta kuma ce daruruwan 'yan kwanta-kwanta, ciki har da masu garkuwa da mutane sun ajiye makamansu.

An dai yi hakan ne bayan rantsuwa da suka sha da alkawarin cewa ba za su koma cutar da jama'a ba.

Babu wata mai jiya mai zaman kanta da ta tabbatar da karfi ko tasirin wadanda suka mika wuyan.

Dubban mutane ne aka kashe sannan aka sace daruruwan shanu a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Baya ga wannan, kasar na kuma fama da rikici tsakanin manoma da makiyaya, da kuma na kabilanci da addini musamman a arewa maso tsakiyar kasar.

Rundunar dai ta ce za ta ci gaba da bibiyar wadannan mutane don tabbatar da tuban na su.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An kiyasta cewa an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira da kuma dubban rayuka

Bayanan hoto,

An shafe shekaru shida Buharin Daji na addabar jihar Zamfara da makwabtanta

Kakakin rundunar ta 'yan sanda ya ce kimanin mutum 700 ne masu satar shanu da sace-sace suka tuba.

A baya dai wadansu jihohin kasar Zamfara da Katsina sun ayyana irin wannan sulhu da masu tayar da kayar bayan, amma kuma daga bisani suka koma ruwa.

Jihohin da lamarin ya fi kamari su ne Zamfara, Katsina, Kaduna da wasu sassan jihar Kano.

A watan da ya gabata ne jami'an tsaro suka kashe Buharin Daji - mutumin da ake zargi da addabar yankin.

Sai dai a makon da ya gabata sai da aka kashe gwamman mutane a wadansu kauyukan jihar Zamfara - lamarin da aka dora kan barayin shanun - wadanda aka ce yaransa ne.