Isra'ila ta jingine yarjejeniyarta da MDD

Yan ci rani a Isra'ila

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan ci rani daga kasashen Afirka a Isra'ila na neman a kyale su su zauna a kasar

Firayi Ministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya dakatar da yarjejeniyar bada iznin zama a kasar ga dubban 'yan Afrika da ke cirani.

A karkashin yarjejeniyar wasu kasashen Turai suma za su bayar da matsaguni ga adadin wadanda ke Isra'ilar.

'Yan sa'o'i bayan tabbatar da yarjejeniyar tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Mista Netanyahu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa zai dakatar da yunkurin.

Ya kuma ce yana bukatar yin nazari sosai akan al'amarin.

Ya kara da cewa ya ji ra'ayoyin 'yan Israila musamman mazauna kudancin Tel Aviv inda dubban 'yan Afirka suke zaune.

Mafi yawa daga cikin 'yan ciranin 'yan Afika fiye da dubu arba'in da aka kiyasta cewa suna Israilar sun fito ne daga kasashen Sudan da Eritriya.

Sun ce sun yi amannar rayuwar su tana cikin hadari matukar aka tasa keyarsu zuwa Afirka.