'Yan sara suka na cin karensu ba babbaka a jihar Kaduna

Gwamna Nasir el-Rufai na ihar Kaduna

Asalin hoton, Facebook/The Governor of Kaduna State

Bayanan hoto,

A baya dai gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa'i ta sha alwashin hukunta duk masu tada zaune tsaye a jihar, ciki har da 'yan sara suka da barayin shanu

Aikata muggan laifuka tsakanin al'umma na ci gaba da zama barazana a wadansu garuruwa na arewacin Najeriya, kamar jihar Kaduna, inda 'yan sara-suka ke cin karensu ba babbaka.

Baya ga matsalar da rikicin Boko Haram ya haddasa na rashin tsaro, wato sabuwar barazanar da ta sake dawowa bayan daukar lokaci da dainawa ita ce matsalar 'yan shara.

Jama'a a wadansu sassa na jahar Kaduna na nuna damuwa kan masu aikata wannan ta'asa.

Ko a kwanan sai da wani fada ya barke a unguwar Kawo tsakanin 'yan sara sukar har ya halaka wani matashi da kuma kone wasu gidaje guda biyu ciki har da gidan Biredi.

Lamarin dai ya zama tamkar gaba kura baya sayaki, dan hatta malamai ba a bar su a baya ba wajen nuna damuwa.

A cewar wani malami hatta cikin masallatai ba su tsira ba, dan akan far wa jama'a da ke sallah ku jiran lokacin sallah da sara da sukar, tare kuma da yi musu kwacen wayar salula, da dan kudadensu.

A wasu lokutan hatta a makabarta akan bi mutanen da suka je binne gawa, a kwace musu kudade.

Wasu na ganin ko da an kama irin wadannan matasa, babu wani hukuncin da ake musu. Hasali ma ba sa daukar lokaci ake sako su, kuma su ci gaba da aikata abin da suka ga dama.

Al'ummar yankin Tudun Wada da su unguwar Kawo sun yi kira ga gwamnatin jihar ta dauki matakin magance matsalar kafin ta yi kamari.

Hukumomi dai na cewa suna kokarin kakkabe wannan matsala,inda yan sanda suka bada shelar cafke wasu ,matasa guda 70 da ake zargi da sara suka, to sai dai wasu na cewa sakin su ake yi ba tare da hukunci ba.