'Yan Shi'a na kara matsa wa gwamnati kan Zakzaky

Asalin hoton, WhatsApp/Saminu
Daruruwan mabiya Shi'a a Najeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim el-lzakzaky sun yi zanga-zanga a tsakiyar birnin Abuja a ranar Laraba.
Masu zanga-zangar sun sauya wurin da suka saba yin taronsu ne bayan 'yan sanda sun mamaye dandalin Unity Fountain, wurin da suka kwashe makwanni suna zaman dirshen.
Injiniya Abdullahi Muhammad Musa wani mabiyin Sheikh Zakzaky ne kuma yana cikin masu zaman dirshan din matsawa gwamnati lambar sako ta saki malamin addinin.
Mabiya darikar Shi'a sun ce sun shafe kwanaki 86 suna zanga-zangar, kuma sun ce sun damu matuka da halin rashin lafiyar da malamin ke ciki.
Har ila yau ya ce "har yanzu akwai alburushin da aka harbe shi a jikinsa da ba a cire ba."
"Sannan idon malamin guda daya ba ya gani sosai da shi, yayin da shi ma mai lafiyar ya fara tabuwa," in ji shi.
Daga nan ya ce gwamnatin Najeriya ba ta mutunta izinin da kotu ta ba da na sakin shi ba, don ba a same shi da laifin komai ba.
Sai dai a nata bangaren gwamnatin Najeriya ta ce tana ba shi kariya ne, sannan ta daukaka kara.