Ghana: Ba mu bai wa Amurka filin kafa sansanin soji ba

Shugaba Nana Akufo Addo
Bayanan hoto,

Batun dai ya janyo zazzafar muhawara a majalisar dokokin Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Akuffo Adoo yace kasar Ghana bata baiwa kasar Amurka damar kafa sansanin soji a kasar ba, kuma babu niyyar yin hakan anan gaba.

Ya cigaba da cewa, yarjejeniyar sojin dak tsakanin kasashen biyu tsohowa ce wadda yanzu ake naman sabuntawa.

Waannan ya biyo bayan gabatar da yayjejeniyar soji tsakanin kasashen biyu Ghana da Amurka wadda janyo cece kuce da tada jijiyar wuya.

A wata bayyanar da yayi a gidan talabijin shugaban ya Allah wadai da mau sukar cewa yarjejeniyar ta shiga sharo ba shanun ikon kasar Ghana, sannan ya kira masu sukar munafukai.

Ya cigaba da cewar yarjejeniyar zata karfafa karfin kare kasar Ghana da habbaka yunkurin duniya na wanzar da zaman lafiya a yammcin Africa.

Yarjejeniyar sojin tsakanin Amurka ta bar baya da kura inda `yan majalisa suka kauracewa zaman yarjejeniyar a gaban majalisar dokoki, sannan aka gudanar da zanga zanga daga Accra babban birnin kasar Ghana.

Wannan hadin kan sojin na zuwa ne a lokacin da masu tsassauran ra`ayin addini suka zafafa kai hare hare a yammacin Africa, dalilin da masana ke ganin yasa Amurka shiga shirin karfafa sojin ta a yankin.