Bata-gari ne 'ke rura'wutar' rikicin Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta aike da sojoji jihar Zamfara don tabbatar da tsaro
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce matsalar rikicin masu satar shanu da ke cigaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi ba za ta rasa nasaba da hannun wasu ba da ba sa son jihar ta zauna lafiya.
Cikin watannin da suka gabata, barayin shanu sun yi ta kai hare-haren da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu.
Sannan an yi hasarar dukiya, ta hanyar cinnawa gidajen mutane wuta a kauyukan da barayin shanun suka kai wa hari.
A 'yan kwankin baya ne dai Senator Sa'idu Dan Sadau ya ce gwamnatin jihar ta kasa a saboda haka ya kamata gwamnan ya sauka.
To amma mai magana da yawun gwamnan jihar kan harkokin yada labarai, Malam Ibrahim Dosara ya shaida wa BBC cewa wasu da ba sa son zaman lafiya su ne suka zagaya ta bayan fage suka bata yarjejeiyar da aka cimma da barayin shanun tun gabannin mutuwar Buharin-Daji.
Ya kara da cewa yaran Buharin-Daji ne suka hallaka shi saboda ya ki ba su hadin kai dan su shiga tattaunawar sulhu da gwamnati.
Dosara ya ce batun da Sanata Dan Sadau ya ke yi na gwamna ya sauka daga mukaminsa dan ya gaza shawo kan matsalar batu ne da ba shi da wani tushe.
Kuma matsalar da jihar Zamfara ke ciki ba ta kai na a ayyana dokar ta baci ba.
Wanda ake zargi da hannu akai harin shi ne Buharin-Daji, wanda kuma aka kashe a cikin watan da ya gabata.
Gwamnatin jihar ta yi bikin murnar mutuwarsa, da fatan an kawo karshen matsalar amma ba a dauki lokaci ba aka ci gaba da kai hare-haren da a cewar wasu yaran Buharin-Daji ne suke daukar fansa kamar yadda ya taba fada ko bayan ransa, sai an dauki watanni 10 yaransa na kai harin daukar fansa gare shi.