Adikon Zamani: Sana'o'in da mata ke iya yi daga gida

Adikon Zamani: Sana'o'in da mata ke iya yi daga gida

"Yin kasuwanci daga cikin gida ya taimaka mini!"

Ana samun karuwa a yawan mata da suke gudanar da harkokokin kasuwancinsu daga cikin gida a maimakon aikin gwamnati ko na kamfani da ake zuwa ofis karfe goma na safe, a tashi karfe biyar na yamma.

Wannan tsari na ci gaba da samun karbuwa saboda zama a gida na bai wa mata isasshen lokacin da kuma yancin kula da gida yadda ya kamata.

Ga wasu kuwa yana taimaka musu wajen shawo kan fargabar da wasu maza masu kishi suke da ita, wadanda ba sa son matansu na mu'amala da mazan da ke waje.

Ga wasu, makudan kudin da ake bukata domin gudanar da harkar kasuwanci a cikin shago ko kasuwa na cikin abubuwan da suke sa su zauna a gida, saboda yana taimaka musu wajen yin riba ba tare da sun kashe kudi sosai ba.

Akasarin masu wannan harka kan yi amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajarsu tare da samun kwastamomi.

Ana ganinsu a shafukan sada zumunta na Instagram da Facebook da kuma Twitter.

A filin Adikon zamani na wannan mako, na tattauna da wasu mata uku wadanda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu daga cikin gidajensu.

Za mu ji kalubalen da suke fuskanta da kuma abubuwan da ya kamata a yi domin harkar kasuwanci ta bunkasa.

Shin kuna ganin ya dace a yi harkar kasuwanci daga cikin gida?