Nigeria: Manoman dankalin Turawa na bukatar tallafi

Dankalin Turawa ci maka ce da kusan kowa ke ci a Najeriya
Image caption Jihohi hudu ne kadai a Najeriya ke noman dankalin Turawa, hakan ya sa ba zai wadata kasa ba bare a fitar da shi kasashen wajen dan samun karin kudin shiga

Manoma dankalin Turawa a Najeriya - sun nemi gwamnatin tarayya da ta rika bauyar da tallafi ta yadda za a habaka noman sa a fadin jihohi talatin da shida da ke kasar.

Manoman sun bayyana cewa a yanzu jihohi biyu zuwa uku ne kadai ke noman sa, wani abu da su ka bayyana cewa shi ne dalilin karancinsa da kuma tsadarsa.

Bincike ya nuna dankalin na Turawa da ake nomawa a Najeriya ya sa mu karbuwa a wasu kasashen Afrika da Turai.

To amma kuma babu wani tanadi na musamman na ketarawa da shi domin samar wa kasar kudade.

A hirar da ya yi da BBC, Alhaji Abdullahi Malami Jos, dan kasuwa kuma manomi ya bayyana cewa har yanzu jihohi ba su hudu ba a Najeriya da ke noman dankalin turawan.

Ya kara da cewa dankalin turawan da Najeriya ke nomawa ya fi wanda ake samu a kasashen turai inganci da kuma kyau.

''Turawan da kansu idan sun zo kasar su kan sayi irin nau'in dankalin mu suka jibga shi a jirgin ruwa su tafi da shi. Ka idan ba shi da inganci babu ta yadda za a yi bature ya yi dakon kaya tun daga Afirka har zuwa kasashe kamar Poland da sauransu,'' inji Abdullahi Malami.

Ya kara da cewa: ''Da gwamnati za ta shigo cikin harkar, ta wadamu da iri da taki mai kyau a matsayin tallafi ko kuma bashi. Tabbas da kowa zai ci gajiyar noman dankalin Turawa, za a samu karin ayyukan yi tsakanin al'uma musamman matasa.''

A karshe ya ce dole ke sanya matasa baro kauyuka su shigo birane dan neman kudi, saboda har yanzu noman da ake yi a kauyuka ba a inganta shi da amfani da fasahar zamani ba dan haka suka gwamnace su fito daga gida su kuma ba zu yankunan Najeriya ciki har da kudancin kasar.

Labarai masu alaka