Rashin ruwa na yin cikas ga noman kankana

Kayan marmari da na lambu
Bayanan hoto,

Kayan marmari da na lambu na da farin jini tsakanin mutanen birane da yankin karkara

Manoma kankana a jamhuriyar Nijar, sun koka da rashin wadataccen ruwan na kawo nakasu ga samar da ita da yawa musamman noman damuna da rani.

Noman kankana na daya daga cikin ayyukan da ke tallafa wa mazauna karkara wajan bunkasa tattalin arzikinsu. To sai dai manoman kankanar na fuskantar matsaloli iri-iri wajan gudanar da ayyukan nasu.

Allah ya albarkaci kasar garin Dan Barde da ke gundumar Magarya a jihar Damagaram ta jumhuriyar Nijar da arzikin noman kankanar, sai dai matsalar rashin wadataccen ruwa ya janyo musu koma baya a wannan fannin.

Shugaban kungiyar manoma kankanar Malam Amir Yussif ya shaidawa BBC cewa gwamnati ce kadai za ta magance musu matsalar da suke fama da ita.

A baya an samar da fanfo guda daya tilo da ake amfani da shi dan yin ban ruwa a lokacin rani, wanda sam bai wadace su ba idan aka kwatanta da yawan kankanar da suke nomawa a lokacin damuna.

''Kan fanfo hudu ka iya sauya yawan kankanar da za mu noma a lokacin rani, saboda haka gwamnati idan ta sanya mu cikin wadanda ake bai wa tallafi na tabbar za a samu gagarumin sauyi ta wannan fanni,'' inji Malamm Amir.

Ya kara da cewa, ''Wani abin farin ciki shi ne, duk kasar da aka noma kankana a wurin tamkar an yi mata sharar hanya ne saboda da an shuka hatsi ko wani nau'i na kayan abinci ba bata lokaci zai fito. Sannan feshin maganin da aka yi wa kasar a lokacin da aka shuka kankana, ya na kare duk wani abu da za a shuka a wurin misali kwari ba za su damu hatsi ba.''

Bukatar kayan marmarin karu a lokacin da watan Azumi ya kama, inda yawancin mutane kan fi son shan 'ya'yan itatuwa a lokacin buda baki. Wanda kankana na daga cikin kayan marmari mai farin jini a wannan lokacin.