Daular Usmaniyya: 'Dan Fodio ya wallafa littattafai fiye da 250'

Fadar Sarkin Musulmi a birnin Sokoto a lokacin da aka yi bikin cika shekara 200 da kafuwar daular a shekarar 2004.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fadar Sarkin Musulmi a birnin Sokoto a lokacin da aka yi bikin cika shekara 200 da kafuwar daular a shekarar 2004

Wani mawallafi littafi akan Daular Usmaniyya ya ce Shehu Usmanu Dan Fodiyo ya wallafa daruruwan littattafai.

Malam Abdullahi Bukhari Sakkwato ne mawallafin littafin "Intellectual Foundation of Sokoto Caliphate", wato Kafa Daular Usmaniyya bisa ilimi da basira.

Ya ce tattara bayanai game da tarihin daular saboda kishi da yake da shi game da sanar da duniya tarihin daular Usmaniyya:

"Littattafan da Dan Fodiyo ya wallafa sun fi 250, illa dai ba a samu tsaresu kamar yadda ya kamata ba, shi yasa wasu suka salwanta."

Malam Abdullahi ya sanar da Sulaiman Ibrahim Katsina na BBC a cikin shirin Taba Kidi Taba Karatu cewa ya yi bincike mai zurfi kafin ya wallafa littafin na shi.

"Na tara bayanai da na samo daga gidan tarihi da kuma gidan Wazirin Sokoto, har ma da sauran masana da ke Sokoto."

Ya bayyana cewa, "A takaice na sami wallafe-wallafe 147 na marigayi shehu Usmanu Dan Fodiyo."

Ya ce ban da wadannan littattafan, ya tattaro bayanai game da tarihin Sarki Musulmi Mahammadu Bello da Abdullahin Gwandu:

"Na tattara bayanai da suke nuna littattafan Sarki musulmi Mahammadu Bello sun kai 180, na Abdullahin Gwandu kuma sun kai 187."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hubbaren Shehu Usman Dan Fodiyo a birnin Sokoto da ke arewacin Najeriya

Tarihin Daular Usmaniyya

Mallam Abdullahi Buhari ya bayyana cewa littafin ya tabo dukkan sassa na tarihin Daular Usmaniyya:

"Wannan littafi ya tabo dalilin jihadi, har zuwa ga tarihin shugabanni ko uwayen da suka kafa daular."

Ya kara da cewa littafin ya tabo wadanda aka fara ba tutocin kafa masarautun daular na farko.

"Wadannan su ne sarakunanmu na arewa su kimanin 17, har ma da shahararrun malamai da suka yi rubuce-rubuce na bunkasa addinin musulunci da siyasa a cikin daular."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu algaita a fadar Sarkin Musulmi da ke Sokoto

Littafin ya kunshi tarihin dukkan sarakunan musulmi tun daga Shehu Usman Dan Fodiyo zuwa kan wanda ya ke kai yanzu.

"Akwai tarihin masarautar Gwandu, har ma da tsarin sarakunan da ke nada sarkin musulmi," inji shi.

Ya bayyana ma BBC cewa ya wallafa littafin ne saboda kishin da yake da shi na Daular Usmaniyya da Shehu Usman Dan Fodiyo ya kafa cikin ilimi da hikima a wannan yanki na Afirka.

Ya kuma ce ya wallafa wannan littafi ne a shekarar 2015, kafin aka wallafa shi daga baya.

Malam Abdullahi Bukhari Sakkwato, na tare da Kwalejin Shehu Shagari da yake Sakkwato a Najeriya.