Ghana: Mutane sun mutu wajen hako ma'adanai

Shugaba Nana Akufo Addo na kasar Ghana

Asalin hoton, Getty Images

Akalla mutane shida sun mutu yayin da wasu biyu kuma suka jikkata bayan wani ramin hako ma`adanai na kamfanin Newmont Ghana da ke Ahafo ya rufta dasu.

Hadarin ya faru ne ranar asabar lokacin da rufin tsohon ramin hako ma`adinan - wanda ake fadadawa ya rufta akan ma`aikatan.

Amma an sallami mutane biyu da suka ji ciwo daga asibiti bayan an duba lafiyarsu.

Kamfanin ya dakatar da ayyukansa, sannan ya kawar da sauran ma`aikatansa daga wurin.

A wata sanarwa da kamfanin ya gabatar, ya bayyana cewa ma`aikatan da suka mutu na aiki ne a kamfanin gine-gine na Consar Limited, wanda yake yi wa kamfanin Newmont din aikin fadada wurin hako ma`adinan.

Ministan Kasa da Ma`adinai, Peter Amewu ya ce gwamnati za ta gudanar da binciken abinda ya janyo faruwar hadarin.

Ana yawan samun irin wannan hadarurruka a wuraren hako ma`adinai ta haramtacciyar hanya a Ghana.

Amma wannan hadarin na bayan nan ya haifar da damuwa game da ingancin tsare-tsare a wuraren hako ma`adinai.