An kwance katafaren bam a Jamus

Sama da mutane dubu ashirin da shida aka kwashe daga yankin kafin kwance bam din. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sama da mutane dubu ashirin da shida aka kwashe daga yankin kafin kwance bam din.

Wata tawagar kwararru a kasar Jamus sun kwance wani katafaren Bam mai girma da aka dasa tun lokacin yakin duniya na biyu a yankin Paderborn da ke yammacin kasar Jamus.

Sama da mutane dubu ashirin da shida aka kwashe daga yankin kafin kwance bam din.

Wakilin BBC ya ce sai da aka yi shiri na musamman kafin a ka kwashe mutanen, kuma bayan da a ka kwance bam din sai a ka loda shi a kan wata babbar mota domin fitar da shi daga garin.

Nauyin bam din da aka ce na Burtaniya ne, ya kai ton daya da digo takwas{1.8}, wanda aka gano a lambun wani gidan iyalai sama da mako guda.

'Yan sanda kuma sun soma janye tsaro daga yankin.

Labarai masu alaka