An haifi jariri shekaru 4 bayan mutuwar iyayensa

Iyayen jaririn dai sun mutu ne a shekarar 2013, kuma an adana kwayayen haihuwar su a cikin kankara da fatan samun da. Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Iyayen jaririn dai sun mutu ne a shekarar 2013, kuma an adana kwayayen haihuwar su a cikin kankara da fatan samun da.

Wasu kafofin watsa labarai a kasar China sun ce an haifi wani jariri shekaru hudu bayan mutuwar iyayen sa a hadarin mota.

Iyayen jaririn dai sun mutu ne a shekarar 2013, kuma an adana kwayayen haihuwar su a cikin kankara da fatan samun da.

Bayan abkuwar hadarin 'yan uwan iyayen da suka mutu sun yi ta tafka shari'a don samun ikon amfani da kwayayen haihuwar.

Rahotannin sun ce an haifi jaririn ne a watan Disamba, inda a ka sanyawa wata mata 'yar kasar Laos kwayayen haihuwar a mahaifarta.

Bayan haihuwar jaririn, kakannin sun gudanar da wasu gwaje-gwaje da su ka tabbatar da cewa jaririn jininsu ne kuma hakan zai ba su ikon rike yaron.

Labarai masu alaka