An rage yanke hukuncin kisa - Amnesty

Rahoton ya ce an iso wata gaba ta sauyi a duniya, wato inda a ke shirin kawar da horo mafi muni kuma mai cike da wulakanci.
Image caption Rahoton ya ce an iso wata gaba ta sauyi a duniya, wato inda a ke shirin kawar da horo mafi muni kuma mai cike da wulakanci.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce adadin mutanen da a ke yankewa hukuncin kisa a duniya ya ragu a bara, idan a ka kwatanta da shekarar 2016.

Kungiyar ta ce hakan zai share fage wajen soke yanke hukuncin kisa kwata-kwata.

Rahoton kungiyar na shekara-shekara ya nuna cewa an yanke hukuncin kisa sau dari tara da casa'in da uku a shekarar 2017, kuma hakan ya nuna an samu raguwar kashi hudu cikin dari idan a ka kwatanta da shekarar 2016.

Kungiyar ta ce mai yiwuwa ainihin adadin ya fi haka, tun da China ta ki bayyana yawan mutanen da ta yankewa hukuncin na kisa.

Kungiyar ta sanar da abubuwan da ta ce nasarori ne, wato raguwar hukuncin kisa a Pakistan da kashi 31 cikin 100 kuma babu wani rahoto da ya bayyana cewa an yi kisa ta hanyar jifa.

A duk fadin duniya, hanyoyi hudu ne a ke amfani da su wajen kisa wato ta hanyar fille kai wanda a Saudiyya kadai a ke hakan, sai ta hanyar rataya, ta hanyar yin allurar guba da kuma ta hanyar harbi.

Rahoton ya nuna cewa kasashe hudu kawai ne su ke hada kashi tamanin da hudu cikin dari na hukuncin kisan, kuma dukkansu kasashen musulmai neinda su ka hada da Iran da Saudiyya da Iraki da kuma Pakistan.

Wasu kasashe goma sha tara su ma sun yanke hukuncin kisan.

Rahoton dai ya kalubalanci kasashen da ke yankewa mutane hukuncin bisa laifukan da ba na tayar da hankali ba ne kamar sayar da kayan sata a China, zina da maita a Saudiyya da kuma yin sabo a Iran da Pakistan.

Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa a cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, Amurka da Japan ne kadai har yanzu su ke yanzke hukuncin ksa, inda kasar Belarus ta kasance tilo cikin kasashen turai da ke yanke hukuncin.

Rahoton ya ce an iso wata gaba ta sauyi a duniya, wato inda a ke shirin kawar da horo mafi muni kuma mai cike da wulakanci.

Labarai masu alaka