Boko Haram ta sace yara fiye da 1000 a Najeriya – UNICEF

Wata makarantar boko da ta zama sansanin 'yan gudun hijirar Boko Haram
Image caption An mayar da wasu makarantun da suka rage sansanonin 'yan gudun hijira, lamarin da ya tilasta wa wasu yaran daina zuwa makaranta

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce fiye da yara 1000 mayakan Boko Haram suka sace a yankin arewa maso gabashin kasar tun daga shekarar 2013.

Asusun ya ce sun gudanar da bincike kan wadanda aka kawo rahoton an sace su, amma kuma adadin ka iya fin haka.

A wani rahoto da UNICEF ta fitar, a wani bangare na taron tunawa da shekara hudu da sace 'yan matan Sakandaren Chibok sama da 200 a jihar Borno, asusun ya ce an ci gaba da kai hare-hare kan yara da sace su.

Rahoton ya ce 'yan Boko Haram sun kashe sama da malaman makaranta 2000, da kuma lalata sama da makarantu 1400 cikin shekara 10 da suka dauka suna kaddamar da hare-hare a Nigeria.

A lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya alkawarin kawo karshen ayyukan masu tayar da kayar baya.

To amma har yanzu Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare kan farar hula, da sojoji da 'yan kato-da-gora a kasar.

Labarai masu alaka