Sai an ba coci kudi ake shiga aljannah- inji Fasto a Najeriya

Pastor Enoch Adeboye Hakkin mallakar hoto PASTOR ADEBOYE/FACEBOOK
Image caption Pastor Enoch Adeboye shugaban cocin Redeem a Najeriya

Jagoran daya daga cikin coci-coci mafi girma a Najeriya ya haifar da rudani a cikin wani wa'azinsa ga mabiya addinin Kirista.

Pastor Enoch Adeboye, wanda shi ne shugaban cocin Redeem na daya daga cikin fastoci ma su arziki a Najeriya.

A cikin wani hoton bidiyonsa da ya mamaye shafukan sada zumunta na intanet, Faston ya ce duk wanda ya ki bayar da kudin sadaka da ake kira baiko ba zai shiga aljanna ba.

Sannan ya bukaci sauran shugabannin rassan cocin su gabatar da sakon ga mabiyansu a lokacin da yake wa'azin.

Kalaman na Mista Adeboye sun haifar da cece-kuce tsakanin mabiya addinin kirista a Najeriya.

Wasu daga cikin mabiyan sun bayyana rashin jin dadi kan yadda ake kokarin mayar da addinin kirista na kudi.

Wasu kuma da ke goyon bayan kalaman na faston sun ce hakan yana cikin karantarwar littafi mai tsarki.

A Najeriya dai ana daukan addini da matukar muhimmanci, inda wasu ke ganin wajibi ne ga mabiya su bayar kudade da sunan sadaka.

Kudaden da ake bukatar mutum ya biya sun shafi ware kaso 10 ga cocin daga cikin kudaden da yake samu.

Wasu mabiya addinin kirista na sukan faston ne bisa tsawwala irin wannan kudi da ake karba a cocinsa, yayin da ake kallon irin dukiyar da shugabannin coci a Najeriya suka mallaka.

Akwai da dama daga cikin malaman coci da suka mallaki jirgin sama.

Sannan manyan coci a Najeriya da kan hada gangamin dubban mutane, wani lokaci da katin ATM ake biyan kudaden baikon.

Labarai masu alaka