Rikicin Mali ya raba mutum 3,000 da matsugunansu

Sabbin 'yan gudun hijira da ake gani a halin yanzu bakaken fata ne 'yan kasar Mali
Image caption Sabbin 'yan gudun hijira da ake gani a halin yanzu bakaken fata ne 'yan kasar Mali

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin da ake fama da shi a Mali ya haddasa karuwar mutanen da ke gudun hijira zuwa wasu kasashe.

Hukumar ta ce ya zuwa yanzu kimanin mutum 3,000 daga kasar ta Mali suka tsere zuwa kasar Burkina Faso mai makwabtaka.

Hukumar ta UNHCR ta ce Sanarwar da fitar dai manuniya ce na irin mawuyacin halin da ake ciki a Mali da kuma yadda rikicin kabilanci ke haddasa gungun jama'a tserewa don neman mafaka.

'Yan gudun hijira na farko daga Mali a shekarar 2012, fararen fata ne 'yan Tuareg da kuma larabawa da suke tsere daga arewaci, kuma suna zaune ne a tsakanin Mauritania da Burkina Faso da kuma jamhuriyar Niger.

Amma sabbin 'yan gudun hijira da ake gani a halin yanzu bakaken fata ne 'yan kasar Mali da suka tsere daga tsakiyar kasar tsakanin kabilun Fulani da 'yan kabilar Dogons, a yankin da ba'a girke dakarun wanzar da zaman lafiya ta MDD ba.

Garuruwan da ke tsakiyar kasar Mali sun hada ne da garin Djenne da kuma Mopti, inda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka ce sojojin na cin zarafi tare da kashe 'yan kabilar Fulani.

Hukumar UNHCR ta ce sabbin 'yan gudun hijiran daga Mali na tserewa zuwa wasu yankunan kasar Burkina Faso da ake karancin abinci.

A shekarar 2012 ne aka fara rikici a Mali bayan da mayakan kungiyar Al-Kaida suka yi amfani da burin neman ballewa da 'yan aware suka yi saboda rashin shugabanci nagari.

Labarai masu alaka