Kun san nasarori da matsalolin da Arsene Wenger ya samu?

Arsene Wenger ya ci kofi biyu har sau biyu a kakar wasanninsa ta farko a matsayin kocin Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsene Wenger ya ci kofi biyu har sau biyu a kakar wasanninsa ta farko

Nasarorin Arsene Wenger

Wenger ya lashe gasar kwallon kafa ta firimiya har sau uku kuma ya dauki kofin gasar kwallon kafa ta FA har sau hudu a kakar wasanni tara da ya yi a jere tun bayan da ya fara aiki a matsayin kocin Arsenal.

A shekarar 2003-04, ya zama koci na farko tun bayan shekarar 1988-89, da ya jagoranci kungiyar kwallon kafar ta Ingila da aka kammala kakar wasanni ba tare da an doketa ba,

Sai dai bayan nasarar da ya yi a gasar cin kofin FA a shekarar 2005, kungiyar ta yi shekara tara ko kuma kwanaki 3,283 kafin ta sake cin wani kofi .

Arsenal ta samu wannan nasarar ce lokacin da ta doke Hull City a gasar cin kofin FA, kafin ta sake cin kofin a kakar wasanni da ta biyo baya.

A kakar wasannin bara ne Arsene Wenger ya ci kofinsa na bakwai a gasar FA , lokacin da Arsenal ta doke Chelsea da ci 2-1, amma sun kammala gasar Firimiya a bayan Chelsea da maki 18.

Image caption Wasu daga ciki shahararun 'yan wasan da suka yi tamaula a Arsenal karkashin jagorancin Wenger

Lokacinda ya fara fuskantar koma baya

Kungiyarsa dai ta rika gwagwarmaya a Turai tun bayan da ta sha kaye a hannun Barcelona a wasan karshe na gasar Zakarun Turai a shekarar 2006.

An fitar da su a wasannin da ya rage kulob-kulob 16 a kakar wasanni ta bakwai da suka yi nasara, kuma shi ne lokaci na karshe da suka bayyana a gasar a shekarar 2017, inda Bayern Munich ta lallasa Arsenal da ci 10-2 jumulla.

A shekarar 2006, suka koma filin wasa na Emirate da aka gina a kan fam miliyan 390 bayan da suka bar Highbury.

Kungiyar Arsenal dai ba ta kashe kudi sosai wajan sayan 'yan wasa kamar sauran kungiyoyin kwallon kafa da suke hammayya da juna a gasar Firimiya ba ,amma sau biyu Wenger yana kafa sabon tarihi wajen sayen 'yan wasa a kakar bana.

Dan wasan gaba na Faransa, Alexandre Lacazette ya koma kungiyar ne a bara kan fam miliyan 46.5, yayin da a watan Janairun da ya gabata ya sayo dan wasan gaba na Gabon, Pierre Emerick Aubameyang a kan fam miliyan 56.

Shin wane ne zai gaji Arsene Wenger ?

Tuni aka danganta tsohon kocin Borussia Dortmund Thomas Tuchel da aikin, duk da cewa shi kansa Wenger ya ce tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal Patrick Vieira ne yake ganin ya yi kama da wanda zai gaje shi.

Ya zuwa yanzu dai Tuchel shi ne wanda ya fi cancanta a wurin masu kungiyar, bayan kocin kungiyar kwallon kafa ta Jamus Joachim Low da tsohon kocin Real Madrid da AC Milan da Chelsea Carlo Ancelotti.

"Burinmu shi ne mu ga mun dora a kan nasarorin da Arsene ya samu lokacin da ya yi aiki, tare da mutunta manufarsa wajen tabattar da cewa Arsenal na cikin kungiyoyin da za su fafata, kuma za ta dauki kofin da ya fi kowanne girma da kuma muhimanci a gasar" in ji Kroenke.

Fitattun 'yan wasan da suka bar Wenger a Arsenal

 • Jens Lehmann: Ya bar Arsenal a 2008 ya koma Stuttgart lokacin da kwantiraginsa ya kare a kungiyar daga baya ya yi ritaya. Ya sake komawa tamaula a 2011 daga nan ya sake shiga Arsenal.
 • Bacary Sagna: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Landan.
 • Kolo Toure: Ya koma Manchester City, bayan shekara bakwai da ya yi a Arsenal.
 • Thomas Vermaelen: A shekarar 2014 ya koma Barcelona.
 • Ashley Cole: Ya koma murza-leda a Stamford Bridge ita kuwa Chelsea ta bayar da William Gallas.
 • Patrick Vieira: Ya koma wasa ne a Juventus.
 • Cesc Fabregas: A shekarar 2003 ya koma murza-leda a Barcelona.
 • Marc Overmars: A shekarar 1997 ya koma Barcelona domin maye gurbin Luis Figo.
 • Alexis Sanchez: Ya koma Old Trafford, inda Manchester United ta bayar da Henrikh Mkhitaryan.
 • Robin van Persie: A shekarar 2012 ya koma murza-leda a Manchester United.
 • Thierry Henry: Ya koma buga tamaula a Barcelona a 2000.
Hakkin mallakar hoto Getty Images