Tunisia ta yi sabuwar dokar da ta raba iko ga kananan hukumomi

Shugaban kasar Mohamed Beji Caid Essebsi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kasar Mohamed Beji Caid Essebsi

Majalisar dokokin Tunisiya ta amince da fara amfani da wata sabuwar doka da za ta raba iko ga kananan hukumomi--dokar da aka shafe shekaru uku ana aiki kan dokar.

Hakan na zuwa ne gabanin zabukkan kananan hukumomi da aka shirya gudanar wa a farkon watan Mayu.

Ana dai kallon zabukkan a matsayin babban ci gaba ga habbakar mulkin demukradiyya a kasar.

Tun da farko an yi ta nuna damuwa cewa 'yan Majalisun dokokin kasar ba zasu kammala aikin zartar da wannan sabuwar doka ba kafin zabukkan kananan hukumomi.

Sai dai bayan shafe shekaru ana tafka muhawara a karshe, fiye da kashi biyu bisa uku na 'yan majalisu sun kada kuri'ar amincewa da dokar.

Manufar dokar dai ita ce hada kananan hukumomi karkashin tsarin dokoki na bai daya wanda zai karfafa rarraba ikon gwamnatin tarayya zuwa matakai daban daban.

Muhimmin dalilin zartar da wannan doka dai shi ne baiwa kananan hukumomi da kuma shugabannin al'umma damar fada a ji kan batutuwan da su ka shafi harkokin kudade.

Ana fatan cewa rarraba iko zai bada damar yin adalci wajen rarraba kasafin kudin kasa zuwa sauran bangarorin da ke matukar bukatar ayyukan ci gaba.

Hakan dai a cewar masu lura da al'amura zai samar da ayyukan ci gaban a yankunan da al'ummomin ke ganin gwamnatin tarayya ta mayar da su saniyar ware.

Kasar Tunisia na daya daga cikin kasashen Musulunci da suke da sassaucin ra'ayi a duniya, kuma ta shahara wajen yadda masu zuwa yawon bude ido daga nahiyar Turai ke rububin zuwa, saboda tekunan da suke kasar.

Labarai masu alaka