'Ganawar Koriya ta share fagen sabon babi'

Shugabannin biyu da matansu Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugabannin biyu sun amince su yi aiki tare

Kafar watsa labarai ta gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayar da rahoton ganawa tsakanin shugaban kasar Kim Jong-un da takwaransa na Koriya ta Kudu Shugaba Moon, inda ta nuna lokacin da shugabannin biyu suka hadu a kan iyaka.

An bayyana lokacin a matsayin wani babban abin tarihi, kuma jaridar gwamnatin kasar ta Koriya ta Arewa ta ce ganawar ta share fagen wani sabon babi a tsakanin kasashen.

Jaridar ta kuma wallafa cikakkiyar yarjejeniyar da shugabannin biyu suka cimma, wadda ta hada da batun raba yankin na Koriya da makaman nukiliya.

Yawancin mutane a Koriya ta Arewa kusan a ce ba su da wata masaniya sosai a game da taron shugabannin biyu in banda yanzu.

Jaridar gwamnatin kasar ta Rodong Shinbum ta wallafa hotuna da yawa sannan ta dan ambato abin da ta bayyana a matsayin matsalar raba yankin Koriyar da makaman kare-dangi.

Tsawon shekara da shekaru gwamnatin Koriya ta Arewa ta kafe cewa ba za ta taba watsi da shirinta na kera makaman nukiliya ba, abin da ta ce tana bukata domin kare kanta daga mamayar Amurka.

Yarjejeniyar da shugabannin biyu suka sanya wa hannu ta bayar da damar da Koriya ta Arewa za ta yi watsi da makaman nata na kare-dangi, bisa sharadin tabbatar mata da tsaro ko kawar mata da wata fargaba ta mamaya ko hari daga mai mara wa Koriya ta Kudu baya wato Amurka.

Sai dai babu cikakken bayani kan yadda za a cimma hakan, illa dai wannan zai rage ne ga Donald Trump kila a ji yadda yake a lokacin ganawarsa da Kim Jong-un a karshe-karshen watan Mayu ko farko-farkon watan Yuni.

Har yanzu jami'an Amurka na shawarar inda za a yi taron shugabannin biyu, amma ana ganin Mongolia da Singapore su ne kasashe biyun da ake duba yuwuwar gudanarwar a daya daga cikinsu.

Labarai masu alaka