Clasico: Ko Real Madrid za ta iya doke Barcelona?

Barcelona da Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta doke Madrid 3-0 a haduwa ta farko a La Liga

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar La liga a karawar hamayya ta Clasico karo na 238 a ranar Lahadi.

Karawar na zuwa a yayin da Barcelona ke cikin shaukin bikin lashe kofin La liga da Copa del Ray, yayin da Real Madrid kuma ke murnar kai wa wasan karshe a gasar zakarun Turai karo na uku a jere.

Real Madrid ta ce ba za ta karrama Barcelona ba a matsayinta na wadda ta lashe kofin La liga kafin fara fafatawar.

Barcelona ta taba karrama Real Madrid a 2008 bayan ta lashe kofin La liga.

Amma Zinedine Zidane ya bayyana rashin jin dadi kan yadda Barcelona ta ki karrama 'yan wasansa bayan sun lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallo kafa.

Wasu na ganin karawar ta ranar Lahadi ba ta da wani muhimmaci, saboda tuni Barcelona ta karbi kofin La liga, kamar yadda Real Madrid ta mayar da hankali ga karawarta da Liverpool a gasar zakarun Turai

Sai dai kuma wasanni hudu suka rage Barcelona ta kammala kaka ba tare da an doke ta ba a La Liga.

Bayan lashe kofin La liga karo na bakwai a shekaru 10 a ranar Lahadin da ta gabata, yanzu abin da Barcelona ta sa a gaba shi ne kammala La Liga ba tare da an doke ta ba.

Barcelona za ta so ta kafa wannan tarihin a gasar La liga a Spain, yayin da kuma Real Madrid za ta nemi hana wa Barcelona kafa tarihin.

A nata bangaren kuma Real Madrid da ke matsayi na uku a tebur, za ta nemi karbe matsayi na biyu ne a hannun Atletico Madrid.

Don haka wasan Clasico a ranar Lahadi zai yi zafi kamar yadda aka saba gani.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda Barcelona ta karrama Madrid a 2008

Tazarar maki 15 Barcelona ta ba Real Madrid kuma za ta so ta kara yawan makin zuwa 18, wanda zai kasance tazara mafi girma da Barcelona ta ba Real Madrid a tarihin hamayyarsu.

Sannan Zidane zai yi kokarin rama kashin da ya sha ci 3-0 a Santiago Bernabeu a hannun Barcelona a watan Disemba.

A ranar 26 ga Mayu ne Real Madrid za ta fafata da Liverpool a wasan karshe a gasar zakarun Turai a birnin Kiev na Ukraine.

Madrid na harin lashe kofin gasar ne karo na 13.

Kaftin din Madrid, Sergio Ramos ya ce idan suka lashe kofin gasar zakarun Turai zai shafe nasarar da Barcelona ta samu na lashe kofuna biyu a Spain.

Sannan ya ce za su bi umurnin kocinsu na kin karrama Barcelona a ranar Lahadi.

A tarihin Clasico, Real Madrid ta samu nasara a karo 95 yayin da Barcelona ta samu nasara karo 93.

Idan har Real ta ci kwallo daya zai kasance kwallo ta 400 da ta ci Barcelona a tarihin Clasico. Barcelona kuma ta ci Real Madrid kwallaye 387.

Wannan haduwar za ta kasance ta 38 ga Andres Iniesta kuma Clasico ta karshe ga Kaftin din na Barcelona kafin ya bar kulub din a karshen kaka.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ce kakar Ernesto Valverde ta farko a Barcelona.

Labarai masu alaka