Zaben shugabannin APC 'ya bar baya da kura'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Me zai faru bayan tarukan jam'iyyar APC?

An gudanar da zaben shugabannin APC a mazabu a sassan Najeriya cikin yanayi na rikici da tashin hankali.

An samu rikici tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a jihohi da dama musamman daga manyan jiga-jigan jam'iyyar da ba a zabi 'yan takararsu ba.

Ko da yake an gudanar da zaben sabbin shugabannin na APC a mazabu a wasu jihohi a ranar Asabar ba tare da an samu rikici ba.

Amma zaben na zuwa a lokacin da APC ke fama da rigingimun cikin gida a rassan jam'iyyar na jihohi da kuma yadda suka yi kamari ba tare da an shawo kansu ba.

APC ta ce ta yaba da yadda aka gudanar da zaben na shugabanninta a mazabu a sassan kasar.

A sanarwar da ta fitar, jam'iyyar ta amsa cewa an samu kura-kurai a wasu waurare inda ta ce ta kafa kwamitin sauraren koken wadanda suke ganin an saba masu.

A jihar Delta dai an kashe daya daga cikin 'yan takarar zaben shugabannin jam'iyyar ta APC mai suna Jeremiah Oghoveta.

Rundunar 'yan sandan jihar da ta tabbtar da faruwar lamarin, ta ce an daba ma sa wuka ne har ya mutu sakamakon takaddama da ta kaure tsakanin bangarorin jam'iyyar ta APC da ke hamayya a karamar hukumar Ughelli.

Wani bangare na jam'iyyar APC a jihar Bauchi kuma ya zargi bangaren gwamna Mohammed Abubakar da hana wa 'yan takararsu fom domin takarar zaben.

A jihar Adamawa an dage gudanar da zaben na shugabannin APC a muzabu da ya kamata a gudanar a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce an dage zaben ne zuwa Lahadi bayan wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun yi zargin cewa 'yan takara da dama ba a ba su damar yankar fom na yin takarar zaben ba.

Adamawa na daya daga cikin jihohin da zaben shugabannin na APC zai iya haifar da rikicin siyasa musamman tsakanin manyan jiga-jiga jam'iyyar a jihar da suka hada da bangaren gwamna da Sanata Abdul'aziz Nyako da Nuhu Ribadu da kuma tsohon sakataren gwamnati Babachir David Lawal.

A jihar Zamfara ma an samu rikici a mazabar Sankalawa karamar hukumar Bungudu.

Wani mazauni yankin, ya shaida wa BBC cewa sai da 'yan sanda suka yi amfani da tiyagas bayan da matasa suka kama jifarsu.

Zamfara ma na cikin jihohin da ke fama da rikicin jam'iyyar APC tsakanin bangaren Sanata Marafa mai wakiltar zamfara ta tsakiya a majalisar dattijai da kuma bangaren gwamna Abdul'aziz Yari.

Sannan rahotanni daga Zamfara sun ce 'yan sanda sun rufe hanyar shiga da fita Gusau babban birnin jihar saboda zaben shugabannin na APC a mazabu a ranar Asabar.

Wasu matafiya da lamarin ya rutsa da su, sun shaida wa BBC cewa sun shafe sama da sa'a biyar a wuri daya kafin jami'an tsaro suka bude hanyar shiga Gusau.

Hakkin mallakar hoto Kabiru Jangebe
Image caption Tun karfe 8 na safe aka rufe hanyar shiga Gusau har karfe 1 na rana

A jihar Rivers, rahotanni sun ce magoya bayan Sanata Magnus Abe sun yi zanga-zanga inda suka hana gudanar da zaben a wasu wurare a Fatakwal.

Bangaren Sanata Abe da ke neman takarar gwamna, sun yi korafi ne kan tsarin zaben tare da sukar shugabannin jam'iyyar musamman yadda aka bari sai a ranar zaben 'yan takarar ke cike fom.

Wannan na zuwa a yayin da a jihar Ekiti aka dage babban zaben fitar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC bayan barkewar rikici.

Rahotanni sun ce wasu matasa sun abka wajen taron suka farfasa akwatunan zaben, tare da zubar da takardun kuri'un da aka kada.

'Yan takara 33 ke neman kujerar gwamnan a APC da suka hada da tsohon gwamnan jihar Kayode Fayemi da kuma tsohon kakakin majalisar jihar Femi Bamisile.

A ranar 14 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben gwamnan na Ekiti, kuma APC na son kwace kujerar ne daga PDP da ke mulkin jihar.

Masharhanta siyasa na ganin rigingimun da APC ke fama da su a jihohi na iya yi wa jam'iyyar illa sosai a zaben 2019.

Wasu 'ya'yan jam'iyyar da suke ganin an saba ma su na iya ficewa zuwa wata jam'iyyar adawa.

Labarai masu alaka