Barcelona da Real Madrid sun yi canjaras 2-2

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lionel Messi ne kan gaba a La Liga da kwallo 33 a kakar wasan bana

Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya saka kwallo ta biyu a ragar Barcelona, wanda ya sa kugiyoyin suka tashi a wasansu na "El Classico" da ci 2 da 2.

Tun da farko Barcelona ta buga da 'yan wasa 10 na tsawon mintuna 45, kuma saura wasanni uku kungiyar ta shafe dukkan kakar wasa ta bana ba a ci ta ba.

Alkalin wasa ya nuna wa Sergio Roberto jan kati a lokacin wasan yana 1 - 1 kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan da alama ya mari dan wasan baya na Real Marcelo.

Amma da farko Roberton ne ya samar da kwallon da Luis Suarez ya jefa a ragar Real kafin Cristiano Ronaldo ya farke cin da Karim Benzema ya yi masa hedin.

Daga baya Lionel Messi ya saka kwallo ta biyu a ragar Real, amma sai Gareth Bale ya farke ta ba tare da bata lokaci ba.

An sauya Ronaldo a lokacin hutun rabin lokaci bayan da ya sami rauni a agararsa a lokacin da ya zura kwallon da ya ci.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Cristiano Ronaldo da Alfredo Stefano ne ke da kwallaye 18 ga kowannensu a wasannin El Classico

Labarai masu alaka