An sa ranar da matan Saudiyya za su fara tukin mota

Saudi women driver Hakkin mallakar hoto Reuters

Kasar Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar 24 ga watan Yuni, matan kasar za su sami izinin fara tukin mota a cikin daular.

Wannan matakin zai kawo karshen hanin tukin mota na shekaru masu yawa a kasa ta karshe a duniya da ta hana mata tukin mota.

Hukumomi sun dauki wannan matakin na kyale matan Saudiyya su fara tukin mota a bara ne.

Kuma a watan Yunin bana aka shirya fara amfani da dokar - amma sai yanzu aka bayyana ainihin ranar da mata za su fara kam kambun motoci.

Wannan matakin shi ne mafi jan hankula a cikin dukkan matakan kawo sauyi da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya dauka a cikin kasar.

Muhimmancin matakin yana da alaka da bunkasa tattalin arzikin kasar ban da kara wa matan daular iko a fannonin rayuwa daban daban.

Cikin dan kankanin lokaci, yawan motocin da ake sayarwa ya karu matuka, kuma makarantun koyar da tukin mota da wasu harkoki masu alaka da sufuri sun bayyana a kowane sashe na Saudiyya - a wani mataki na shirya wa isowar wannan ranar mai cike da tarihi.

Wasu malaman addini da a da suka ce jikin mata ba shi da juriya kuma kwakwalwarsu ba zata iya daukan kwaranniyar tuki ba sun fito yanzu suna cewa samun mata masu tukin mota a titunan kasar zai inganta yanayin tuki.

Labarai masu alaka