Indiya: Walmart ya sayi Flipkart akan $16bn

Alamar kamfanin Flipkart Hakkin mallakar hoto Reuters

A wani mataki na kasuwanci da zuba jari da zai kasance mafi girma a kasar Indiya, kamfanin Walmart ya sanar da cewa zai sayi wani bangare da zai mallaka masa kamfanin Flipkart na Indiya.

Wannan cinikin zai ba Walmart damar ja da kamfanin Amazon a daya daga cikin kasuwanni mafi girma da saurin bunkasa a duniya.

Bayan fiye da shekara guda ana tattaunawa, kamfanin Walmart na dab da sayen kashi 77 cikin dari na hannayen jarin kamfanin Flipkart a kan dala biliyan 16.

An dai kafa kamfanin na Flipkart a 2007, a lokacin ya fara da sayar da littatafai ta intanet ne.

Amma tuni ya bunkasa inda ya shiga cikin kasuwancin kayan sawa da kayan lantarki da kayan kwalliya da na shafe-shafe.

Wadanda suka kafa kamfanin sun kasance wasu abin kwatance a fagen kasuwanci ta intanet a Indiya.

Wannan cinikin zai kara bunkasa kudaden shiga ga kamfanin, kuma zai taimaka masa fadada ayyukansa zuwa wasu sassa na kasuwanci kamar na kayayyakin masarufi.

Ga kamfanin Walmart kuwa, wannan wata dama ce ta shiga kasar Indiya.

Dokokin Indiya sun takaita kokarin kamfanin na shiga kasar ya gina maka-makan shaguna kawo yanzu.

Wannan cinikin kuma na nufin cewa kamfanin na Walmart zai rika karawa da na Amazon a Indiya kenan.

Amazon ya fara shiga Indiya a 2012, kuma yana kan gaba wajen kasuwanci salon na intanet a kasar.

Labarai masu alaka