Barcelona za ta kawo ziyara nahiyar Afirka

Magoya bayan zakarun Afirka ta Kudu Mamelodi Sundowns Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne karo na biyu da zakarun Afirka ta Kudu Mamelodi Sundowns suka gayyato Barcelona

Barcelona ta tabbatar da cewa za ta buga wasan sada zumunta da zakarun Lig na Afirka ta Kudu, Mamelodi Sundowns.

Za a yi wasan ne a ranar 16 ga watan Mayu.

Sundowns ne suka fara sanar da wasan a makon da ya gabata amma an dauki lokaci kafin a karkare yadda abubuwan za su kasance.

Kuma hakan ne ya sa aka fara nuna shakku kan ko wasan zai gudana ko kuma a'a.

Sai dai Barcelona ta tabbatar da karawar a shafukanta na sada zumunta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan zai bai wa magoya baya damar kallon fitattun 'yan wasa gaba-da -gaba kamar irinsu Lionel Messi

Kulob din na Afirka ta Kudu ya kuma yi nasarar shawo kan Horoya na Guinea da Hukumar Kwallon Afirka ta CAF su dage wasan da ya kamata su yi na gasar zakarun Afirka da mako daya.

Wasan wanda za a yi a Soccer City, da ke wajen birnin Johannesburg, shi ne karo na biyu da Sundowns ta gayyato zakarun na Spaniya domin wasan sada zumunta.

Barcelona na da ragowar wasa biyu a kakar bana inda ta ke kokarin kammala gasar La Liga ba tare da an doke ta ba.

Za su kara da Levante ranar Lahadi, sannan kuma da Real Sociedad bayan mako guda, yayin da za su je Afirka ta Kudun a tsakanin wadannan wasannin.

Labarai masu alaka