Malaysia: An saki Anwar Ibrahim daga gidan kaso

Anwar Ibrahim of Malaysia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon firaiministan Malaysia Anwar Ibrahim

An saki tsohon shugaban 'yan hamayya Malaysia, Anwar Ibrahim, wanda ya samu afuwa daga sarkin kasar Sultan Muhammad V.

Shekara Uku data wuce aka daure shi a karo na biyu, wanda ya ce kasafi ne laifin da aka ce ya yi.

Mista Anwar, mai shekara 70, shekara 20 data gabata aka aike shi gidan yari na farko, zamanin Friministan Mahathir Mohamad, wanda ya kore shi daga gwamnatinsa.

Yanzu kuma da sukayi sulhu, mutane biyu suyi aiki tare wajen samun nasarar mamaki a zaben kasar makon daya gabata, wanda ya kawo karshan mulki jam'iyya mai mulki a karo farko.

Mista Mahathir yace zai sauka ya bar wa Anwar mulki a ciki shekara biyu mai zuwa.

Mista Anwar dai yana da yakinin cewa Malaysia na kan turbar sabon babi sauyi, duk da cewa demokradiya na fuskantar koma baya a wasu wurare.

Labarai masu alaka