Limaman Cocin Katolika za su fuskanci hukunci

Pope Francis Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wasu limaman Cocin Katolika fiye da 14 a kasashen Austaralia da Chile na fuskantar hukunci bayan da ta fito fili cewa sun shafe shekaru suna yin lalata da kananan yara.

Wani fitaccen limamin katolika, Archbishop na birnin Adelaide, Philip Wilson shi ne fada mafi girman mukami da aka samu da laifin boye laifukan yin lalata da kananan yara, bayan da wata kotu a yankin New South Wales ta yanke masa hukunci.

Ban da Australiya ma, an sami aukuwar irin wannan aika-aikar a kasar Chile.

An dai tuhumi Archibishop din ne da boye aukuwar lalata da kananan yara da wani limamin cocin na katolika ya rika yi a yankin na New South Wales a shekarun 1970.

Philip Wilson, wanda ya taba rike wani mukami a cocin a wancan lokacin na iya shafe shakara biyu a gidan yari.

Lauyoyinsa sun ce ba shi da masaniya game da laifukan yin lalata da wani fada da ke aiki a karkashinsa ya aikata, wanda kuma aka samu da laifin yin hakan daga bayan har aka daure shi a kurkuku, inda ya mutu a shekarar 2006.

Amma wani majistire ya ce hujjojin da aka gabatar a kotu masu inganci ne.

Matsalar tana fadada

A kasar Chile ma an dakatar da wasu limaman cocin na katolika su 14 bayan da bincike ya gano cewa sun aikata lalata da kananan yara.

A lokacin da yake bayyana matakin da aka dauka na ladabtar da limaman, Bishop din birnin Rancagua, Alejandro Goić , ya nemi afuwa domin rashin daukar wani mataki akan mutumin bayan da wata mata ta sanar da shi game abin da ya kira "halayyar da ba ta kamata ba" da limaman cocin ke nunawa a gundumarsa.

A sakamakon wannan abin kunyar, Bishop Goic da wasu limamai 34 daga kasar ta Chile sun mika takardun yin murabus bayan da Fafaroma Francis ya kira su a fadar Vatican da ke birnin Rome, domin ya duba jerin koke-koke da ke fitowa daga sassa daban-daban na cocin.