Mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya yi murabus

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi Nuhu Gidado
Bayanan hoto,

Kawo yanzu Injiniya Nuhu Gidado bai bayyana abin da zai yi nan gaba ba

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Injiniya Nuhu Gidado ya yi murabus daga mukaminsa, kuma tuni Gwamna Muhammad Abubakar ya amince da matakin.

A cikin wasikar da ya mika wa gwamnan a ranar Laraba, ya ce da ma bai yi niyyar "wuce wa'adin mulki daya ba akan wannan mukamin".

Sannan ya kara da cewa a yanzu "ba shi da karsashin aikin, kuma ci gaba da zama a kan kujerar ba adalci ba ne ga gwamnan, da mukamin, da kuma shi kansa".

Murabus din Injiniya Gidado ya zo ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari a jihar ta Bauchi bayan zaben shugabannin jam'iyyar APC mai mulki da aka yi.

Daga baya, gwamnan na Bauchi Muhammad Abubakar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya amince da murabus din Malam Gidado.

Sannan ya kara da cewa ya dauki tsohon mataimakin nasa da "muhimmanci a gwamnatinsa".

"Ina yi masa fatan alheri kan al'amuran da zai tunkara nan gaba kuma na yi alkawarin ba shi dukkan goyon bayan da yake bukata a kowanne lokaci.

"Ina kuma fatan cewa zai amsa kira a nan gaba idan aka neme shi ya byaar da gudummawa domin ci gaban jihar Bauchi," in ji Gwamna Abubakar.

Gwamna M A Abubakar ya tabbatar da karbar takardar murabus din mataimakin nasa ne a shafinsa na Twitter:

"A yau na karbi takardar murabus din Mataimakin Gwamna Injiniya @NUHUGIDADO. A madadin jama'ar jihar Bauchi, ina yi masa godiya kan aikin da ya yi a lokacin da ya ke ofis."

Kawo yanzu Injiniya Nuhu Gidado bai bayyana abin da zai yi nan gaba ba.

Zaben shugabannin jam'iyyar APC da aka yi a 'yan kwanakin baya dai ya kara fito da rabuwar kan da ke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar a jihar.

Ana samun takun-saka tsakanin magoya bayan Gwamna Abubakar da kuma 'yan majalisun tarayya daga jihar karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

Masu adawa da gwamnan na zarginsa da kaucewa akidar jam'iyyar APC da kasa tabuka komai a tsawon shekara ukun da ya shafe a kan mulki.

Sai dai gwamnan da magoya bayansa sun sha musanta wannan zargi, suna cewa siyasa ce kawai.

Jihar ta Bauchi dai na daya daga cikin wuraren da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ke neman wa'adi na biyu a zaben 2019, ke da goyon baya sosai.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin matukar ba a shawo kan rikicin ba, to jam'iyyar za ta iya fuskantar koma baya a zaben na badi.

Karanta karin wasu labaran