Rikicin Birnin Gwari na bazuwa zuwa makwabtan garuruwa

Cattle rustling Hakkin mallakar hoto Getty Images

'Yan fashin shanu da suka koma satar jama'a don neman kudin fansa na tsallakawa zuwa wasu makwabtan kananan hukumomi a jihar Kaduna.

Rahotanni na cewa wasu mahara sun kai mamaya yankin Kidandan na karamar hukumar Giwa dauke da manyan makamai inda suka yi awon gaba da shanu sama da dari biyar.

Wani mazaunin yankin ya fada wa BBC yadda maharan suka kai harin a yankinsu na Kidandan a wayewar garin Alhamis.

"Da safen nan ne muke ta jin harbe-harbe, ashe irin masu sace shanu ne suka zo mana".

Ya kara da cewa: "Kimanin shanun zasu kai 500, akalla ba akasara ba".

Haka zalika, bayanai na cewa 'yan fashin na ci gaba da satar mutane don neman kudin fansa a yankin Birnin Gwari.

Shugaban kungiyar ma'aikatan motocin sufuri yankin Birnin Gwari, Mallam Danladi Idon Duniya ya ce da maraicen ranar Laraba ma an sace mutum uku a tsakanin kauyen Maganda zuwa Birnin Gwari.

"Mutum uku ne suka dauka, ireba daya, fasinja biyu, kuma an fara magana da su, kuma sun ce a kawo miliyan biyar. To har yanzu ba akai karshe an shirya da su ba tukun"

A nata bangaren gwamnati ta ce tana iya kokarinta wajen kawo karshen wannan iftila'i.

Kanar Yusuf Soja shi ne mataimaki na musammam ga gwamnatin jihar Kaduna kan sha'anin tsaro:

"Babu wanda zai ce wannan abin na faruwa kuma bai dame shi ba.

Kanar Yusuf ya kuma ce, 'Bi izinillahi, cikin dan lokaci kadan abubuwan da ke faruwa a yankin Birnin Gwari da wani yanki na Giwa zai zamo tarihi."