Ana tuhumar Google da Facebook da taka dokar kare bayanai

Max Schrems, Austrian lawyer and privacy activist, who is the head of new NGO 'None of Your Business' (NYOB).

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Max Schrems shugaban kungiyar 'None of Your Business' (NYOB)

An kai karar kamfanonin Facebook da Google da Instagram da kuma WhatsApp sa'o'i kadan bayan da sabuwar dokar kare bayanan nan ta GDPR ta fara aiki a fadin Tarayyar Turai.

Ana tuhumar kamfanonin ne da tilasta wa masu amfani da shafukan sada zumunta da su amince da a rika amfani da bayanansu wajen aika musu da talla, ko kuma a fitar da su daga shafukan.

Wata kungiya mai suna None of Your Business (NYOB.eu) ta ce kamfanonin na hana wa mautane zabin da sabuwar dokar ta tabbatar musu.

Idan aka same su da laifi, dole ne kamfanonin su sauya yadda suke aiki, kuma ana iya cin su tara.

Wannan sabuwar dokar ta General Data Protection Regulation (wato GDPR) ta fayyace sabbin hanyoyin da za a rika sarrafa bayanan sirri na mutane da aka tattara da kuma yadda za a rika amfani da su.

Dole ne dukkan kamfanoni da hukumomi a Tarayyar Turai su sauya yadda suke tafiyar da ayyukansu na tattara bayanai ko da kuwa suna wajen tarayyar Turai ne, idan dai suna son cigaba da yin hulda da jama'a a yankin.

Kungiyar Noyb.eu ta ce kamfanonin Facebook da Google da Instagram da kuma WhatsApp sun karya wasu sassa na sabuwar dokar, saboda suna tsare-tsare na tilastawa masu amfani da shafukansu su amince da sababbin tsare-tsaren da suka fitar ko kuma su dode su baki daya daga amfani da shafukan.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kungiyar wadda ke fafutukar kare hakkokin jama'a a intanet ta kuma ce dole ne kamfanonin su ba mutane zabin yadda ake tattara bayanansu da amfani da shi musamman wajen tallace-tallace, ta yadda idan masu amfani da shafukan basu gamsu ba, suna iya rufe shafukansu.

'Yan asalin tarayyar Turai hudu ne dai suka shigar da wannan karar a kasashen Austria da Belgium da Faransa da kuma Jamus.

A sanadiyyar sabuwar dokar, wasu kamfanoni sun dakatar da ayyukansu a fadin tarayyar ta Turai don gudun taka sabuwar dokar.

Kuma dukkan kamfanin da aka samu da laifi a karkashin dokar ta GDPR, za a iya cinsa tarar fiye da fam mliliyan 17.

A nata bangaren, kamfanin Facebook ya ce ya shafe wata 18 yana shiryawa domin fuskantar wannan sabon tsarin.

Shi kuma kamfanin Google ya ce zai cigaba da kokarin yin biyayya ga sabuwar dokar, amma kamfanoni kamar WhatsApp basu ce komai ba kawo yanzu.

Batun bayanan sirri na masu amfani da intanet na jan hankulan al'umma a fadin duniya tun bayan badakkalar nan ta Cambridge Analytica da ta yi amfani da bayanan miliyoyin mutane domin karkatar da ra'ayinsu dangane da zabuka, musamman a Amurka, Turai da kuma Najeriya.