Kotu ta daure wasu 'yan awaren Kamaru

'Yankin Ambazonia na fafutikar wariyar da suka ce ana nuna musu a Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan yankin Ambazonia na fafitikar kawo karshen wariyar da suka ce ana nuna musu a Kamaru

Wata kotun Kamaru ta yanke hukuncin daurin shekara 10 zuwa 15 a kan wasu masu fafutika su 7 daga yankin masu amfanin da turancin Ingilishi, da ta ce, ta samu da laifin ingiza tawaye da ta'addanci.

Cikin wadanda aka yanke wa hukunci, hadda wani mai gabatar da shiri a gidan rediyo, Mancho Bibixy, a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wannan na zuwa ne, bayan a jiya Juma'a, rahotanni daga garin Menka ke tabbatar da gano gawarwakin wasu matasa maza su 9, wanda mazauna yankin ke zargin jami'an soji da kashe su.

Tun a shekarar da ta gabata, rashin zaman lafiya ya tsananta a yankin arewaci, da masu turancin Ingilishi ke da rinjaye a Kamaru, bayan da 'yan tawaye suka dau doka a hannu su.

Akwai mutane da dama da suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma sun yi gudun hijira.