Spaniya: Firai minista Mariano Rajoy na fuskantar kiranye

Spain PM Mariano Rajoy Hakkin mallakar hoto Getty Images

A yau ne 'yan majalisa a Spaniya za su yi mahawara akan ko su tsige firai ministan kasar Mariano Rahoy daga mukaminsa, bayan wani gagarumin badakkalar da ta shafi jam'iyyarsa mai mulkin kasar.

Wannan zaman majalisar ya zo gabanin kuri'ar yanke kauna da za su kada, wanda ka iya kawo karshen mulkin Mista Rahoy.

Spaniya na cikin rikicin siyasa da ya mamaye kasar, banda rikicin yankin Catalonia da yaki ci, yaki cinyewa.

An sami jam'iyya mai mulkin kasar ta Popular Party da hannaye dumu-dumu a wata badakkalar cin hanci da rashawa - wanda aka lakaba wa suna "The Gurtel Affair" da turancin Ingilishi.

An sami fiye da tsofaffin jami'an jam'iyyar 12, wadanda suka hada da tsohon Ma'ajin jam'iyyar da laifukan karbar cin hanci daga masu neman kwangiloli daga gwamnati.

A makon jiya babbar kotun Spaniya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ta Popular Party ta gina wa cin hanci da rashawa gidan zama a kasar.

Firai minista Mariano Rajoy ya musanta cewa yana da hannu cikin badakkalar, kuma ya dage cewa batu ne da ya riga ya wuce.

Jam'iyyar 'yan adawa ta Socialist ta shigar da wani kuduri na neman a kada kuri'ar yanke kauna a majalisa, kuma sun nemi da a mika musu mulki na wucin gadi domin su shirya zabe.

Labarai masu alaka