Matashi zai shafe shekara 7 a kurkuku saboda fyade

Ghana's President Akfuffo Addo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kasar Ghana Nana Akuffo Addo

Wata kotu a Ghana ta yankewa wani matashi dan shekara 20 zaman gidan yari na shekara bakwai, sannan da aiki mai tsanani saboda laifin aikata fyade.

Kotun ta sami Earnest Asare da laifin kasancewa daya daga cikin gungun matasan da suka yi wa wata yarinya fyade a bara, wanda bidiyon ya bazu a kafofin sada zumunta.

Earnest Asare na daya daga cikin gungun matasan nan da wani bidiyon su ya karade shafukan sada zumunta a shekarar da ta wuce, musamman a shafukan WhatsApp da Facebook, na yadda suka yi wa wata `yar yarinya fyade.

Sauran matasan da aka same su da laifi amma suke da karancin shekaru, an tura karararrakin su zuwa wata karamar kotu.

A cikin bidiyon ya nuna yadda yaran suka danne wata `yar yarinyar akan wani benchi, inda suka yi ta amfani da ita daya bayan daya.

Dadin dadawa suna ihu suna shewa suna jin dadi, lamarin da janyo mummunan suka da cece kuce, yayin da wasu suka bukaci a bima yarinyar hakkinta.

Kamar a wasu kasashen Afrika, fyade ba wani sabon abu ba ne, sai dai sabon abu shi ne yadda yanzu aka fara yada bidiyon a shafukan sada zumunta.

Labarai masu alaka