Zinedine Zidane ya sanar da barin Real Madrid

Real Madrid boss Zinedine Zidane

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sau hudu Zinedine Zidane yana lashe Kofin Zakarun Turai - sau uku a matsayin koci da sau daya a matsayin dan wasa

Zinedine Zidane ya sanar da cewa zai ajiye aikin horar da Real Madrid, kwana biyar bayan ya lashe Kofin Zakarun Turai a karo na uku a jere.

Zidane ya sanar da matakin ajiye aikinsa a wani taron manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce "abubuwa sun canza kuma dalilin da ya sa na dauki wannan matakin, kulub din yana bukatar wani salo na daban" a cewarsa.

Zidane wanda ya karbi aikin horar da Real Madrid a watan Janairun 2016 ya fice bayan ya jagoranci kungiyar ga nasarar lashe Kofin Zakarun Turai karo uku a jere da kofin La liga guda daya.

Ya ce Ral Madrid kungiya ce da ya ke "matukar kauna."

Zidane mai shekara 45, ya fara jan ragamar kungiyar ne bayan tafiyar Rafael Benitez. Kuma ya jagoranci kungiyar ta samu nasara a wasannin 104, ya buga kunnen doki a wasanni a 29 da kuma lashe manyan kofuna tara.

Sai dai kungiyar Madrid ta kasance a mataki na uku ne a kakar La Ligar bana wato maki 17 tsakaninta da abokiyar hamayyarta Barcelona.

Zidane ya taba cewa zai tafi a watan Fabrairu "idan ya ga babu wani sabon sauyi da zai kawo a kungiyar".

Sanarwar barin aikin ta zo wa mutanen da yawa da ba-zata saboda yadda ta zo kwanaki kadan bayan doke Liverpool da ci 3-1 a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.

Karanta wadansu karin labarai