Kungiyar ma'aikatan lafiya ta janye yajin aiki

Man on strike Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar ma'aikatan lafiya a Najeriya ta sanar da janye yajin aikin da ta tsunduma a kasar kusan mako 6, wanda ya kusan gurgunta asibitocin kasar.

Matakin janye yajin aikin na zuwa ne, bayan kotun ma'aikata ta alkawarta shiga tsakanin masu yajin aikin da gwamnati.

Ma'aikatan jinya da ungozoma da sauran kwararu a fanin kiwon lafiya--banda likitoci--sun bukaci karin albashi da inganta musu walwala.

Babban sakataren kungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, Kwamared Shettima Ahmed Thomas ne ya sanar da wannan.

Ya ce, "Mun janye yajin aikin bisa umarnin kotun ma'aikat, wato Industrial Court.

Amma ya kara da cewa za su sanar da mambobin kungiyar halin da ake ciki, kuma su masu biyayya ga doka da oda ne.

Ana kyautata zaton rayuwar marasa lafiya ta fada cikin hatsari wasu ma sun rasa rayukansu sakamakon wannan yajin aiki.

Cikin kwananki uku masu zuwa ake sa ran ma'aikatan su koma bakin aikinsu.

Labarai masu alaka