An hana shigar da tsofaffin motocin hawa

Shugaban Yuganda Yoweri Museveni yana amsa waya Hakkin mallakar hoto UGANDAN GOVERNMENT

Majalisar kasar Yuganda ta kafa wata doka da ta hana shigar da motocin da suka wuce shekaru 15 da kerawa.

Wannan dokar na son yaki da gurbata yanayi da kuma hadurra daga tsofaffin motocin.

Rage gurbatar yanayi da inganta yanayin tukinmota sun zama wasu manyan batutuwa a Yuganda.

Gwamnatin kasar ta sanar da kwanaki uku na zaman makok bayan wani mummunar hadarin mota da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum ashirin a karshen makon jiya.

Binciken da aka gudanar na baya-bayan nan ya nuna cewa birnin Kampala na cikin biranen Afirka mafi gurbatar yanayi.

Amma masu shigar da motoci cikin kasar sun ce hana shigar da motocin da suka wuce shekara 15 da kerawa zai janyo karuwar rashin aikin yi.

Sun kuma ce 'yan kasar za su fuskanci matsaloli wajen sayen sababbin ababen hawa saboda tsadarsu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Yuganda Yoweri Museveni

A Uganda, akan sanya wa sabuwar mota harajin kashi 50 cikin dari na ainihin farashinta.

Domin a rage tsadar sabbin motocin, 'yan majalisar kasar sun cire wani haraji da aka sanya wa motocin da basu wuce shekara 8 da aka kerasu ba.

A bara, 'yan Uganda sun shigar da kimanin tsofaffin motoci 2.500 a kowane wata. A makwabciyar kasar, Kenya, ma an hana shigar da motocin da suka gota shekara 8 da kerawa.

To amma sai Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya sanya hannu kafin sabuwar dokar ta kama aiki a farkon watan Yuli.

Labarai masu alaka