Razan al Najar: Dubbai sun halarci jana'izar ma'aikaciyar jinya

Palestinian mourners carry the body of Razan al-Najar during her funeral in Khan Younis, southern Gaza Strip, 2 June 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Gawar Razan al-Najar kenan a lokacin da dubban Falasdinawa suka taru don birne ta

Dubban Falasdinawa sun halarci janazar wata ma'aikaciyar jinya mai aikin jin kai da sojojin Isra'ila suka kashe a lokacin wata zanga-zangar da aka yi a birnin Gaza kusa da iyakar Isra'ila a ranar Juma'a.

Ma'aikatan kiwon lafiya da shaidu sun ce an harbe Razan al-Najar mai shekara 21 ne a lokacin da ta ke kokarin kai dauki ga wani Bafalasdine da aka raunata.

Lamarin ya auku ne kusa da shingen da ya raba Gaza da Isra'ila.

An shafe makonni Falasdinawa a Gaza na birne 'yan uwansu da dakarun Isra'ila suka kashe a yayin da suke zanga-zanga a kusa da iyakar da ta rabba yankin da Isra'ila.

Kuma batun cewa Razan al-Najar ma'aikaciyar kiwon lafiya ce ya kara wa masu zanga-zangar karfin gwuiwa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahaifinta ya je wajen janazar da farar rigar 'yar tasa da ke da jininta

Mahaifinta ya je wajen janazar da farar rigar 'yar tasa da ke da jininta, inda mahaifiyarta kuma ke neman a bi masu hakkinsu.

Mahaifiyar Razan ta ce, "Da gangar aka kashe min 'ya ta... da gangar aka kashe ta."

Sojojin Isra'ila sun ce za su binciki yadda aka kashe ta.

Labarai masu alaka