'Trump zai iya yafewa kansa-da-kansa' kan binciken Rasha

Rudy Giuliani Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rudy Giuliani ya ce Shugaban Trump ba zai yi hakan ba duk da cewa yana da dama

Lauyan Shugaban Amurka ya ce watakila Shugaban na da ikon yi wa kansa afuwa idan har a ka kama shi da wasu laifuka a binciken da a ke yi na sa hannun Rasha a zaben shugaban kasar na shekarar 2016.

Amma Rudy Giuliani ya cewa babu wani dalili da zai sa shugaban ya yi wa kansa lamunin tunda bai aikata wani laifi ba.

Ya kuma ce Shugaba Trump ba zai yi wa kansa afuwa ba domin hankali ba zai dauka ba kuma hakan na iya sa wa a tsige shi.

Haka kuma, Mr Giuliani ya ce babu tabbas a kan ko Mr Trump zai amince a tattauna da shi, a wani fanni na binciken da Lauya na musamman Robert Mueller ke yi.

Sai dai da alama, lauyoyin Shugaban za su hana shi bayar da shaida.

Labarai masu alaka