An fara bai wa matan Saudiyya lasisin tukin mota

A baya sai iyali sun dauki hayar direban da zai rika fita da 'yanuwansu mata. Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption A baya sai iyali sun dauki hayar direban da zai rika fita da 'yanuwansu mata.

Ma'aikatar yada labaran kasar Saudiyya ta sanar da cewa a ranar Talata ne aka fara bai wa matan kasar 10 katin shaidar iya tuka mota bayan sun musanya takardun shaidarsu na kasar waje zuwa na kasarsu, a wani lamari mai cike da tarihi a kasar.

Wadannan mata dai su ne rukunin farko da suka fara karbar 'yancin shaidar tuka mota, tun bayan da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman al-Sa'ud ya fara gabatar da sauye-sauye a kasar.

A baya, dokokin Saudiyya sun bukaci mata su rika neman izinin maza kan wasu shawarwari ko mataki, kuma hana mata tuki na daya daga cikinsu, wannan na nufin cewa sai iyali sun dauki hayar direban da zai rika fita da 'yanuwansu mata.

Ana sa ran mata za su yi tururuwa zuwa ofishin da ke kula da fannin katin shaidar iya tukin mota don samar musu shaidar da za ta fara aiki ranar 24 ga watan nan.

Kafin wannan mataki dai, Saudiyya ce kadai kasar da ba ta amince mata su tuka mota ba a duniya.

Labarai masu alaka