Kada a saki jiki wajen shawo kan Ebola a DRC- WHO

Ma'aikatan lafiyar kasar dubu biyu ne a ka yi wa riga kafin cutar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'aikatan lafiyar kasar dubu biyu ne a ka yi wa riga kafin cutar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya yi gargadi kan kada a saki jiki bisa barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo. Lokacin da ya kai ziyara kasar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, duk da dai akwai alamomin da ke nuna cewa an fara shawo kan annobar, har yanzu ba ta gushe ba.

Cutar ta kashe mutane saba'in da biyu a lardin Equator tun farkon bullarta a watan jiya, amma ba a sake samun wani da ya kamu da cutar ba tun ranar shidda ga watan Yuni.

Ma'aikatan lafiyar kasar dubu biyu ne a ka yi wa riga kafin cutar, wacce kuma gwaje-gwaje su ka nuna alfanunta.

Cutar Ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrika a shekarar 2014.

Wannan dai shi ne karo na 9 da ake samu bullar Ebola a Congo tun shekara ta 1967.