Me ya sa ba za a dagewa Koriya ta Arewa takunkumi ba?

Sakataren harkokin wajen Amurka Mr Pompeo tare da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da Japan

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Sakataren harkokin wajen Amurka Mr Pompeo tare da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da Japan

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce ba za a dagewa Koriya ta Arewa duk wani takunkumi ba, har sai ta soke shirinta na nukiliya kwata-kwata. Mr Pompeo ya yi wannan bayani ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi a Seoul tare da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da kuma Japan. Sakataren harkokin wajen ya ce Pyongyang a shirye ta ke ta soke shirinta na nukiliyar.

Taron da suka yi yazo ne kwanaki bayan ganawa mai dumbin tarihi da Shugaba Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jung-un suka yi a Singapore. Shugabannin sun sanya hannu a kan wata takarda inda suka yi alkawarin kulla sabuwar dangantaka a tsakaninsu.

Koriya ta Arewa dai ta kara tabbatar da cewa za ta cika alkawurran da ta dauka na soke shirinta na nukiliya kwata-kwata a yankin Koriya. Masu nazari dai sun nuna shakku akan wannan yarjejeniya da aka cimma, inda suka ce akwai lauje cikin nadi wajen yadda Koriya ta Arewar za ta soke shirin nata domin ba ta yi cikakken bayani a kan hanyoyin da zata bi ba wajen sokewar da kuma yadda za a gane ta soke din.

Dama dai tunda farko shugaba Trump ya ce Koriya ta Arewar zata kasance cikin takunkumin, har sai ta soke shirinta na nukiliya. Mr Pompeo dai ya je Koriya ta Kudu ne domin sanar da kawayenta na yankin Koriya yarjejeniyar da aka cimman, da kuma sanarwar ba zata da shugaba Trump ya yi na cewa zai tsayar da duk wani aiki na rundunar hadin gwiwa tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu lamarin da ke matukar ciwa Koriya ta Arewa tuwo a kwarya.