Ana samun karuwar mata masu shan tabar wiwi

Ana samun karuwar mata 'yan sama da shekara 40 da ke shan tabar wiwi Hakkin mallakar hoto Image copyrightDIEGO_CERVO

Wani bincike da aka yi a jami'ar York, ya gano cewa ana samun karuwar shan tabar wiwi a tsakanin matan da suka haura shekara 40.

A shekara 10 da ta wuce, yawan matan da ke bayyana damuwarsu a kan ta'ammali da tabar a cibiyoyin lafiya ya rubanya daga 471 zuwa 1008.

Masu bincike sun dora alhakin karuwar da ake samun a kan wadatar kwayar wiwin, inda kuma suke kira da a samar da maganin da zai sa a daina shan tabar wiwin.

To sai dai kuma har yanzu, an fi samun matasa maza da suke ta'ammali da tabat wiwi.

Tabar wiwi dai na da araha da kuma saukin samu, hakan ya bayar da dama ga mutane ke samun ta har ma su yi amfani da ita.

Hakkin mallakar hoto MARLO74

Mutane da dama dai na ganin cewa tabar wiwi ba ta zama jiki ga masu ta'ammali da ita.

Wasu matan dai na shan tabar wiwin ne a mastayin magani, yayin da wasu kuma suka mayar da ita wata kwaya da idan ba su sha ba ba sa jin dadi.

Karanta wasu karin labaran