Habasha da Somaliya na son farfado da dangantakarsu

Firai ministan Habasha Abiy Ahmed Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai ministan Habasha Abiy Ahmed

Firai ministan Habasha, Abiy Ahmed na ziyara a birnin Mogadishu na Somaliya, inda zai tattauna da shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo.

Ana kallon wannan ziyarar a matsayin wani matakin sake gina dangantaka tsakanin makwabtan biyu da suka dade suna zaman doya da manja.

Firai minista Abiy Ahmed na kokarin inganta dangantaka da Masar da Eritriya, kuma ya saki fursunonin da ake tsare da su saboda dalilan siyasa domin domin kawo zamna lumana a kasar.

Babban batun da firai minista Abiy Ahmed zai tattauna da shugaban Somaliya a Mogadishu shi ne na tsaro.

Sojojin Habasha na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da kungiyar masu tayar da kayar baya na al Shabab, amma duk da haka kasashen biyu sun dade suna zaman zulumi.

Wannan ne ma dalilin da yasa yawancin 'yan Somaliya ke kallon sojojin Habashan a matsayin dakarun kasashen waje masu kokarin mamaye kasarsu.

Saboda haka firai minista Abiy zai yi kokarin mika sakon zaman lafiya da hadin kai ga dukkan 'yan Somaliya, matakin da yake fatan zai bunkasa yanayin da ake ciki a kasarsa.

Labarai masu alaka