Shugaba Donald Trump 'sakarai ne' - Xinhua

Shugaba Xi Jinping na China Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Xi Jinping na China

Kafofin watsa labaran China sun soki shugaban Amurka Donald Trump saboda shawarar da ya yanke ta saka harajin kashi 25 cikin 100 akan kayayyakin da China ke shigarwa Amurka.

Kafofin watsa labarai na karkashin kulawar gwamnati ne, kuma ba kasafai suke raba gari da gwamnatin kasar ba.

Saboda haka babu mamaki da kamfanin dillacin labarai na China, Xinhua ya soki Mista Trump kai tsaye.

A wani sharhi da ta fitar, kamfanin dillancin labaran ya ce, "Shugaba mai basira gina gadoji yake yi, amma sakarai kuwa gina katanga yake yi".

Ita kuma jaridar Global Times cewa ta yi shugaban na Amurka na lalata tsarin zamantakewa tsakanin kasa da kasa ne domin ya dadadawa masu goyon bayansa na cikin gida, wadanda - a cewar jaridar - suna ganin kamar yana kare muradunsu ne.

Jaridar People's Daily ma ba ta kyale shugaba Trump ba, domin ta bayyana matakan da ya dauka a matsayin abin kunya. Amma jaridar China Daily ta ce tangal-tangal din da ya ke yi akan muhimman abubuwa na nufin cewa bai san inda ya nufa ba, saboda haka ta shwarci China ta jinkirta mayar da martani.

Saboda matakan na maka wa China harajin kashi 25 cikin dari, hukumomin kasar sun ce nan ba da jimawa ba suma za su saka wa wasu kayayyakin Amurka da take shigarwa China haraji mai yawa.

Labarai masu alaka