Iyalan gida daya da direba sun mutu a hatsari

Hatsarin ababen hawa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saboda cunkoso da rashin kyawun hanyoyi akan sami aukuwar hadurra masu yawa

A ranar Lahadi wani mutum da iyalansa suka gamu da ajalinsu a wani hadari mai sosa rai.

Mutumin mai suna Kamalu, na tare da matarsa Surayya da 'ya'yansu biyu 'yan mata, daya mai shekara biyu daya kuma mai wata takwas.

Sun fito daga Maidile za su unguwa Uku gidan iyayen matar a birnin Kano domin yin gaisuwar Sallah cikin wata keken a daidaita sahu a lokacin da hatsarin ya auku.

Sun isa daidai Western Bypass sai wata babbar mota trela ta bi ta kan keken da suke ciki.

A sanadiyyar hadarin dukkan iyalan gida dayan suka mutu nan take har da direban keken.

Labarai masu alaka