An kai karar ministan tsaro kotun koli

Tun 1979 Shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema ke mulkin kasar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun 1979 Shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema ke mulkin kasar

Rahotanni daga Equatorial Guniea na cewa Babbar jam'iyyar adawar kasar ta shigar da kara a gaban kotun kolin kasar inda ta ke zargin ministan tsaro, Nicolas Obama Nchama, da 'yansanda da azbatarwa.

Wasu takardu da kamfanin dilanci labaran Faransa ya gani, na cewa jam'iyyar ta Citizens Innovation ta zargi cewa akwai mambobi sama da 100 da aka bada umarni a ci zarafinsu ta hanyar gallazawa tsakanin karshen watan Disamba 2017 zuwa farko watan Janairu 2018.

An cafke su ne bayan wani gangamin adawa a watan Nuwamban bara kuma ake rike dasu a ofishin 'yansanda da ke birnin Malabo.

Hotunan da aka gabatarwa kotu sun nuna irin raunin da aka jima mutanen.

Sai dai Mahukuntan Guinea a baya sun taba musanta wannan zargi.

Labarai masu alaka