OPCW: Birtaniya na son a fallasa masu laifi

Firai ministan Birtaniya, Theresa May

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Firai ministan Birtaniya Theresa May

Birtaniya za ta fuskanci tirjiya daga Rasha a yau bayan ta nemi kasashen da ke cikin kungiyar OPCW mai kula da laifukan amfani da makamai masu guba a duniya.

Ta na neman a kara ma sufetocin hukumar ikon fallasa dukkan masu laifin amfani da irin wadannan makaman.

Sakataren harkokin waje na kasar, Boris Johnson zai yi amfani da damar wani taro na musamman da zai gudana a birnin Hague domin shigara da bukatun na Birtaniya, bukatun da Rasha ke adawa da su

A 'yan shekarun nan, tsarin kasa da kasa da yayi hani ga amfani da makamai masu guba ya lalace. An yi amfani da irin wadannna makaman a Syria da birnin Salisbury.

Hukumar OPCW ce ke da alhakin bincikar irin wadannan hare-haren, amma ba ta da izinin gano wanda ya aikata laifukan yaki na amfani da wadannan makaman, sai dai kawai ta gani idan an yi amfani da makaman na guba.

Akan haka ne sakataren harkokin waje na Birtaniya, Boris Johnson zai gabatar da wasu sabbin shawarwari don ba sufetocin hukumar karin ikon da zai sa su iya binciken wadanda ke da hannu idan hakan ya sake faruwa na gaba.

Za a duba wadannan sabbin bukatun a wani taro na musamman da zai gudana a birnin Hague, a gaban dukkan kasashen da suka rattaba hannu akan yarjejeniyar da ta kafa hukumar ta OPCW.

Jami'an diflomasiyyar Birtaniya suna ta zawarcin kasashe masau dama domin ganin sauye-sauyen sun sami karbuwa da zarar an gabatar da su a wajen taron na gobe Laraba.

Amma Rasha tna adawa da wannan shirin wanda ka iya janyo ma kawayenta karin suka da zubewar mutunci a idanun duniya.