Zabiya za su tsaya takara a zaben shugaban kasar Malawi

Wata zabiya a Malawi
Bayanan hoto,

Zabiya

Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito cewa zabiya shida za su tsaya takarar neman shugaban kasa a zaben da za a yi a Malawi.

"Muna so mu nunawa jama'a cewa muna da basira ". Shugaban kungiyar zabiya a kasar malawi, Mr. Overstone Kondowe ya fada wa shafin intanet The Guardian

Kungiyar Zabiya ta yi alkawarin gabatar da 'yan takara shida a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki saboda ya yi amanar cewa wannan zai sauya ra'ayin jama'a a kan zabiya.

A Malawi kamar sauran kasashen yankin, ana farautar zabiya saboda sun yi intifakin cewa ana samun sa'a da kuma arziki idan an yi tsafi da sassan jikinsu .

A shekara 2016 wani kwarare a Majalisar dinkin duniya ya yi gargadin cewa zabiya 10,000 da ke Malawi na fuskantar barazanar "karewa daga doron kasa"idan aka ci gaba da kashesu saboda sasan jikinsu.

Masu aikata miyagun laifi kan tono kaburburan zabiya bayan an binne su domin su sachi kasusuwansu su sayar.

Masu fafituka sun ce talauci yana kara tunzura zaton da ake yi a kan cewa ana samun makkudan kudi daga sassan jikin zabiya .