Kalli hotunan wasu daga cikin wadanda rikicin Filato ya shafa

Wadansu daga cikin wadanda suka jikkata a hare-haren da aka kai wasu kauyuka 11 na jihar Filato suna asibiti inda ake ba su kulawa.

Wani shugaban al'umma a jihar ya shaida wa BBC cewa akalla mutum 200 aka kashe, amma 'yan sanda sun ce 86 ne suka rasa rayukansu.

Sannan wasu da dama ba a san adadinsu ba sun samu raunuka.

Bayanan hoto,

Wasu daga cikinsu na cikin mawuayacin hali

Bayanan hoto,

Wadanda lamarin ya shafa sun fara bayar da labarin yadda aka kai harin

Bayanan hoto,

Yayin da 'yan sanda ke cewa mutum 86 suka mutu a hare-haren, wani dan majalisa a yankin ya ce adadin mutanen ya haura 200

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun ce sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a hare-haren

Bayanan hoto,

Mataimakin shugaban kasa ya nemi hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA da ta tallafa wa wadanda da lamarin ya shafa

Bayanan hoto,

Ita kuwa gwamnatin jihar ta ce tana kokarin sasanta jama'arta ta yadda za a samu irin zaman lafiyar da aka samu a baya

Bayanan hoto,

Wadanda suke tafiya akan hanya ma ba su tsira daga rikicin ba